Yesu ya amsa masa ya ce, “Mafi girma shi ne, ‘Ku saurara, ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukkan ƙarfinka.’ Mabiyinsa shi ne, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’ Ba fa sauran wani umarni da ya fi waɗannan girma.”