1
Yah 10:10
Littafi Mai Tsarki
Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
Porovnať
Preskúmať Yah 10:10
2
Yah 10:11
Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin.
Preskúmať Yah 10:11
3
Yah 10:27
Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.
Preskúmať Yah 10:27
4
Yah 10:28
Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.
Preskúmať Yah 10:28
5
Yah 10:9
Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.
Preskúmať Yah 10:9
6
Yah 10:14
Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni
Preskúmať Yah 10:14
7
Yah 10:29-30
Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban. Ni da Uba ɗaya muke.”
Preskúmať Yah 10:29-30
8
Yah 10:15
kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin.
Preskúmať Yah 10:15
9
Yah 10:18
Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”
Preskúmať Yah 10:18
10
Yah 10:7
Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.
Preskúmať Yah 10:7
11
Yah 10:12
Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran.
Preskúmať Yah 10:12
12
Yah 10:1
“Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.
Preskúmať Yah 10:1
Domov
Biblia
Plány
Videá