1
Luk 8:15
Littafi Mai Tsarki
Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.
Compară
Explorează Luk 8:15
2
Luk 8:14
Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.
Explorează Luk 8:14
3
Luk 8:13
Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.
Explorează Luk 8:13
4
Luk 8:25
Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”
Explorează Luk 8:25
5
Luk 8:12
Waɗanda suka fāɗi a hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa'an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto.
Explorează Luk 8:12
6
Luk 8:17
Ba abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. Ba kuma asirin da ba zai tonu ya zama bayyananne ba.
Explorează Luk 8:17
7
Luk 8:47-48
Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama'a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take. Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
Explorează Luk 8:47-48
8
Luk 8:24
Suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, mun hallaka!” Ya farka, ya tsawata wa iskar da kuma haukan ruwa. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit.
Explorează Luk 8:24
Acasă
Biblia
Planuri
Videoclipuri