1
Luk 17:19
Littafi Mai Tsarki
Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”
Compară
Explorează Luk 17:19
2
Luk 17:4
Ko ya yi maka laifi sau bakwai rana ɗaya, sa'an nan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, ‘Na tuba,’ sai ka yafe shi.”
Explorează Luk 17:4
3
Luk 17:15-16
Ɗayansu kuma da ganin an warkar da shi, ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi, ya fāɗi a gaban Yesu, yana gode masa. Shi kuwa Basamariye ne.
Explorează Luk 17:15-16
4
Luk 17:3
Ku kula da kanku fa. In ɗan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi.
Explorează Luk 17:3
5
Luk 17:17
Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran?
Explorează Luk 17:17
6
Luk 17:6
Ubangiji kuwa ya ce, “Da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da za ku ce wa wannan durumi, ‘Ka ciru, ka dasu cikin teku,’ sai kuwa ya bi umarninku.”
Explorează Luk 17:6
7
Luk 17:33
Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa, adana shi ya yi.
Explorează Luk 17:33
8
Luk 17:1-2
Sai ya ce wa almajiransa, “Sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadinsu! Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku.
Explorează Luk 17:1-2
9
Luk 17:26-27
Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Ɗan Mutum. Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, Ruwan Tsufana kuma ya zo, ya hallaka su duka.
Explorează Luk 17:26-27
Acasă
Biblia
Planuri
Videoclipuri