Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi. Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”