Yakubu ya yi wa'adi da cewa, “Idan Allah zai kasance tare da ni, ya kiyaye ni cikin tafiyan nan da nake yi, ya kuma ba ni abincin da zan ci, da suturar da zan sa, har kuma in sāke komowa gidan mahaifina da salama, da Ubangiji ya zama Allahna, wannan dutse kuwa wanda na kafa shi al'amudi zai zama wurin sujada ga Allah. Daga cikin dukan abin da ya ba ni, zan ba shi ushirinsa.”