Da UBANGIJI ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.
“Muddin duniya tana nan,
lokacin shuki da na girbi,
lokacin sanyi da na zafi,
lokacin damina da na rani,
dare da rana
ba za su daina ba.”