1
Far 11:6-7
Littafi Mai Tsarki
Ubangiji kuwa ya ce, “Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su. Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna.”
Palyginti
Naršyti Far 11:6-7
2
Far 11:4
Sai suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya.”
Naršyti Far 11:4
3
Far 11:9
Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.
Naršyti Far 11:9
4
Far 11:1
A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.
Naršyti Far 11:1
5
Far 11:5
Ubangiji kuwa ya sauko ya ga birnin da hasumiyar da 'yan adam suka gina.
Naršyti Far 11:5
6
Far 11:8
Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya, sai suka daina gina birnin.
Naršyti Far 11:8
Pradžia
Biblija
Planai
Vaizdo įrašai