Luk 21:25-27
Luk 21:25-27 HAU
“Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al'ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa. Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargaban al'amuran da suke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. A sa'an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.