Yah 16:22-23

Yah 16:22-23 HAU

Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku. A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana.