Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa ka yi kusa da keken dokin nan.” Sai Filibus ya yi gudu zuwa wurinsa, ya ji shi yana karatun littafin Annabi Ishaya. Ya ce, “Kana kuwa fahimtar abin da kake karantawa?” Sai ya ce, “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau su zauna tare.