YouVersion Logo
Search Icon

Luk 4:5-8

Luk 4:5-8 HAU

Sai Iblis ya kai shi wani wuri a bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkokin duniya a ƙyiftawar ido. Iblis ya ce masa, “Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, nakan kuma bayar ga duk wanda na ga dama. In kuwa za ka yi mini sujada, duk su zama naka.” Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa, “ ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”