Λογότυπο YouVersion
Εικονίδιο αναζήτησης

Far 6:1-4

Far 6:1-4 HAU

Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi 'ya'ya mata, sai 'ya'yan Allah suka ga 'yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.” A waɗannan kwanaki kuwa, 'ya'yan Allah suka shiga wurin 'yan matan mutane, suka kuwa haifa musu 'ya'ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.