Mat 6:16-18
Mat 6:16-18 HAU
“In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan. Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska, don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”