Mat 20:26-28
Mat 20:26-28 HAU
Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku, kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”