Amos 7:14-15
Amos 7:14-15 HAU
Sai Amos ya amsa ya ce, “Ni ba annabi ba ne. Wannan ba aikina ba ne. Ni makiyayi ne, mai kuma lura da itatuwan ɓaure. Amma Ubangiji ya raba ni da aikina na kiwo, ya umarce ni in tafi in yi magana da jama'arsa, wato Isra'ila.