A.M 3:7-8
A.M 3:7-8 HAU
Sai Bitrus ya kama hannunsa na dama, ya tashe shi. Nan tāke ƙafafunsa da wuyan sawunsa suka yi ƙarfi. Wuf, sai ya zabura, ya miƙe tsaye, ya fara tafiya, ya shiga Haikalin tare da su, yana tafe, yana tsalle, yana kuma yabon Allah.