1Sam 3:9-10
1Sam 3:9-10 HAU
saboda haka Eli ya ce wa Sama'ila ya koma ya kwanta, idan an sāke kiransa sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.” Sama'ila kuwa ya koma ya kwanta. Ubangiji kuma ya zo ya tsaya, ya yi kira kamar dā, ya ce, “Sama'ila! Sama'ila!” Sama'ila ya amsa ya ce, “Ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.”