Luka 17:1-2
Luka 17:1-2 SRK
Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa. Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi.