1
Mat 7:7
Littafi Mai Tsarki
“Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.
Compare
Explore Mat 7:7
2
Mat 7:8
Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.
Explore Mat 7:8
3
Mat 7:24
“Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.
Explore Mat 7:24
4
Mat 7:12
Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”
Explore Mat 7:12
5
Mat 7:14
Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”
Explore Mat 7:14
6
Mat 7:13
“Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa.
Explore Mat 7:13
7
Mat 7:11
To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?
Explore Mat 7:11
8
Mat 7:1-2
“Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku. Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.
Explore Mat 7:1-2
9
Mat 7:26
Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi.
Explore Mat 7:26
10
Mat 7:3-4
Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba? Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan'wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido?
Explore Mat 7:3-4
11
Mat 7:15-16
“Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa. Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?
Explore Mat 7:15-16
12
Mat 7:17
Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan 'ya'ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya.
Explore Mat 7:17
13
Mat 7:18
Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan 'ya'ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan 'ya'ya.
Explore Mat 7:18
14
Mat 7:19
Duk itacen da ba ya 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.
Explore Mat 7:19
Home
Bible
Plans
Videos