1
Mat 23:11
Littafi Mai Tsarki
Amma wanda yake babba a cikinku shi zai zama baranku.
Compare
Explore Mat 23:11
2
Mat 23:12
Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.
Explore Mat 23:12
3
Mat 23:23
“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.
Explore Mat 23:23
4
Mat 23:25
“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari.
Explore Mat 23:25
5
Mat 23:37
“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!
Explore Mat 23:37
6
Mat 23:28
Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.
Explore Mat 23:28
Home
Bible
Plans
Videos