1
Mat 19:26
Littafi Mai Tsarki
Amma Yesu ya dube su, ya ce musu, “Ga mutane kam, ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.”
Compare
Explore Mat 19:26
2
Mat 19:6
Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne. Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”
Explore Mat 19:6
3
Mat 19:4-5
Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karantawa ba, cewa, wanda ya halicce su tun farko, dā ma ya yi su, namiji da tamata?” Ya kuma ce, “Don haka fa sai mutum ya bar uwa tasa da ubansa, ya manne wa mata tasa. Haka su biyun nan su zama jiki guda.
Explore Mat 19:4-5
4
Mat 19:14
Yesu kuwa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Sama na irinsu ne.”
Explore Mat 19:14
5
Mat 19:30
Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”
Explore Mat 19:30
6
Mat 19:29
Kowa ya bar gidaje, ko 'yan'uwa mata, ko 'yan'uwa maza, ko uwa, ko uba, ko 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu ɗari, ya kuma gāji rai madawwami.
Explore Mat 19:29
7
Mat 19:21
Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”
Explore Mat 19:21
8
Mat 19:17
Sai ya ce masa, “Don me kake tambayata a kan abin da yake nagari? Ai, Managarci ɗaya ne. In kuwa kana so ka sami wannan rai, to, ka kiyaye umarnan nan.”
Explore Mat 19:17
9
Mat 19:24
Har wa yau ina gaya muku, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”
Explore Mat 19:24
10
Mat 19:9
Ina kuma gaya muku, kowa ya saki mata tasa, in ba a kan laifin zina ba, ya kuma auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”
Explore Mat 19:9
11
Mat 19:23
Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Hakika, ina gaya muku, da wuya mai arziki ya sami shiga Mulkin Sama.
Explore Mat 19:23
Home
Bible
Plans
Videos