1
Far 37:5
Littafi Mai Tsarki
Yusufu ya yi mafarki. Sa'ad da ya faɗa wa 'yan'uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.
Compare
Explore Far 37:5
2
Far 37:3
Isra'ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da kowannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado.
Explore Far 37:3
3
Far 37:4
Amma sa'ad da 'yan'uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.
Explore Far 37:4
4
Far 37:9
Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa 'yan'uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”
Explore Far 37:9
5
Far 37:11
'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.
Explore Far 37:11
6
Far 37:6-7
Ya ce musu, “Ku ji irin mafarkin da na yi. Ga shi, muna ɗaurin dammuna cikin gona, ga kuwa damina ya tashi tsaye kyam, ga kuma dammunanku suka taru kewaye da shi, suka sunkuya wa damina.”
Explore Far 37:6-7
7
Far 37:20
Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa'an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa'an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.”
Explore Far 37:20
8
Far 37:28
Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma'ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.
Explore Far 37:28
9
Far 37:19
Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa.
Explore Far 37:19
10
Far 37:18
Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi.
Explore Far 37:18
11
Far 37:22
Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyan nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu.
Explore Far 37:22
Home
Bible
Plans
Videos