Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. Kowa ya ci, ya ƙoshi, almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.