1
Mattiyu 7:7
Sabon Rai Don Kowa 2020
“Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.
Compare
Explore Mattiyu 7:7
2
Mattiyu 7:8
Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.
Explore Mattiyu 7:8
3
Mattiyu 7:24
“Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.
Explore Mattiyu 7:24
4
Mattiyu 7:12
Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.
Explore Mattiyu 7:12
5
Mattiyu 7:14
Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.
Explore Mattiyu 7:14
6
Mattiyu 7:13
“Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa.
Explore Mattiyu 7:13
7
Mattiyu 7:11
In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!
Explore Mattiyu 7:11
8
Mattiyu 7:1-2
“Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma. Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.
Explore Mattiyu 7:1-2
9
Mattiyu 7:26
Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.
Explore Mattiyu 7:26
10
Mattiyu 7:3-4
“Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido? Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido?
Explore Mattiyu 7:3-4
11
Mattiyu 7:15-16
“Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?
Explore Mattiyu 7:15-16
12
Mattiyu 7:17
Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.
Explore Mattiyu 7:17
13
Mattiyu 7:18
Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.
Explore Mattiyu 7:18
14
Mattiyu 7:19
Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta.
Explore Mattiyu 7:19
Home
Bible
Plans
Videos