1
Malaki 3:10
Sabon Rai Don Kowa 2020
Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji UBANGIJI Maɗaukaki.
Compare
Explore Malaki 3:10
2
Malaki 3:11-12
Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji UBANGIJI Maɗaukaki. “Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji UBANGIJI Maɗaukaki.
Explore Malaki 3:11-12
3
Malaki 3:17-18
“A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata, za su zama nawa,” in ji UBANGIJI Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima. Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.
Explore Malaki 3:17-18
4
Malaki 3:1
“Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya UBANGIJI wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji UBANGIJI Maɗaukaki.
Explore Malaki 3:1
YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy
Home
Bible
Plans
Videos