Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke. Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.”
Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake bin sa, “Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Isra’ila ba.”