“Addu’ata ba saboda masu bina kaɗai ba ne. Ina addu’a kuma saboda waɗanda za su gaskata da ni ta wurin maganarsu. Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni.