Mar 6:41-43
Mar 6:41-43 HAU
Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka ɗauki kwando goma sha biyu cike da gutsattsarin gurasar da na kifin.