1
Far 3:6
Littafi Mai Tsarki
Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci.
قارن
اكتشف Far 3:6
2
Far 3:1
Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itacen da yake a gonar ba?’ ”
اكتشف Far 3:1
3
Far 3:15
Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”
اكتشف Far 3:15
4
Far 3:16
Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”
اكتشف Far 3:16
5
Far 3:19
Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.” (2Tas 3.10; Far 2.7; Zab 90.3; 104.29; M.Had 12.7)
اكتشف Far 3:19
6
Far 3:17
Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.
اكتشف Far 3:17
7
Far 3:11
Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?”
اكتشف Far 3:11
8
Far 3:24
Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.
اكتشف Far 3:24
9
Far 3:20
Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa'u, domin ita ce uwar 'yan adam.
اكتشف Far 3:20
الصفحة الرئيسية
الكتاب المقدس
خطط
فيديوهات